Hanyoyin Ginin Labari a Cikin Littafin Magana Jari Ce: Nazari a Cikin Littafi Na Farko

Umar Aliyu Bunza & Abdurrahman Faruk

Abstract


Hanyoyin ginin labari wasu fasahohi da masu bayar da labari na baka ko rubutacce ke amfani da su wajen ginawa da tsara labarai yadda labaran za su yi daɗi ga kunnen mai sauraro ko zuciyar mai karatu. A ganin Todorov (1969), ba labari ko abin da labarin ya ƙunsa ke da matuƙar muhimmanci wajen nazarin ba, hanyoyin da aka bi aka bayar da shi. Ke nan kowane labari yana kai bantensa ne ta fuskar hanya ko hanyoyin da aka bi aka bayar da shi. Manufar wannan takarda ita ce nazarin wasu hanyoyin ginin labari da ke cikin littafin Magana Jari Ce Littafi Na Farko na Abubakar Imam. An karanta littafin, sannan aka yi sharhin wasu hanyoyin ginin labarin da mawallafin ya yi amfana da su wajen rubuta labarinsa. Daga ƙarshe, takardar ta gano cewa wasu hanyoyin ginin labarin da Imam ya yi amfani da su a cikin wannan littafi, ya kwaikwaye su ne daga littattafan da ubangidansa R. M. East ya tattara masa na labaran wasu al’ummomi kamar Larabawa da Turawa da mutanen Rasha da Indiyawa da sauransu, shi kuma ya karanta.

Full Text:

PDF

Refbacks

  • There are currently no refbacks.


Â